TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

LAMARI YA BACI

   Subahanallah.


LAMARI YA BACI

Matasa 76 ne Aka kama sun shirya Bikin Auren Jinsi, Luwadi da Madigo a jihar Gombe.

_______________


Hukumar Sibul Difens ta NSCDC a jihar Gombe ta bayyana cewa dakarunta sun kama mutum 76 da ake zargi ‘yan luwadi ne a jihar.


Shugaban hukumar MohammedMu’azu ya sanar da haka ranar Lahadi.


Mu’azu ya ce daga cikin mutum 76 din da aka kama akwai maza 59 da a cikinsu akwai 21 da suka tabbatar wa jami’an tsaron cewa su ‘yan luwad1 ne sannan da mata masu madigo 17.


Ya ce sun kama wadannan mutane a Duwa plaza dake hanyar Bauchi zuwa Gombe yayin da suke taron tunawa zagayowar ranar haihuwa da daurin auren mambobin su.


Mu’azu ya ce zai mai da wadannan mutane da suka kama makaranta yadda ba za su samu lokacin aikata muggan aiyukka irin haka ba.



Daga nan kuma ya ce da zaran sun kammala bincike za a kai su kotu domin yanke musu hukunci.


Kuna Ganin yaya akeyi irin wannan kungiyar ke karfi cikin alumma ba tare da  an Sani ba.......?


Post a Comment

0 Comments