TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Real Madrid na zawarcin Kepa, Chelsea na harin Wirtz

 


gg

ASALIN HOTON

Real Madrid a shirye take ta kulla yarjejeniya ta dindindin da ɗan wasan Chelsea Kepa Arrizabalaga, amma ba za a biya kudin da ya zarta fam miliyan 17.5 ba kan matashin mai shekara 25 da ke tsaron raga a Chelsea kan yarjejeniyar shekara biyar ta fam miliyan 71.6. (Sun)

Juventus za ta yi amfani da rarar kudin da ta samu na albashin ɗan wasan Faransa Paul Pogba mai shekara 30 wajen dauko aron Thomas Partey daga Arsenal a watan Janairu. Pogba na fuskantar haramcin wasanni na tsawon lokaci abin da ya yi tasiri wajen rage albashinsa a Juve.(Mirror)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya sa sunayen 'yan wasan tsakiya Martin Zubimendi na Real Socieded mai shekara 24 da Aurelien Tchouameni, mai shekara 23 daga Real Madrid da Faransa cikin wadanda ya ke hari. (Calciomercato - in Spanish)

Ɗan wasan tsakiya a Fluminense Andre ya ce ya yanke shawarar barin kungiyar a karshen kaka amma kuma a shirye yake ya karbi sabon tayi. Liverpool dai na nuna zawarcinta kan ɗan wasan mai shekara 22. (Mirror)

Chelsea na son cimma yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya a Jamus Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen yayinda ita ma Manchester City ke nuna kwadayinta kan matashin mai shekara 20. (Express)

Chelsea ta tura wakilai domin sa ido kan ɗan wasan Georgia da Valencia da ke tsaron raga Giorgi Mamardashvili, mai shekara 23, a fafatawarsu da Granada ta ranar Lahadi. (90min)

Kocinb Chelsea Blues Mauricio Pochettino na zawarcin mai tsaron raga a Athletic Bilbao ɗan kasar Sifaniya Unai Simon, mai shekara 26. (Fichajes - in Spanish)

Napoli a shirye take ta tattauna sabon kwantiragi da ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen da ake cewa Liverpool na farauta ido rufe. (Fichajes - in Spanish)

Ɗan wasan Chelsea da Ingila Trevor Chalobah, mai shekara 24, ya ja hankalin Borussia Dortmund. (The Sun)

Mai buga gaba a Ingila Divin Mubama, mai shekara 19, ya yi watsi da bukatar tsawaita zamansa a West Ham. (The Athletic - subscription required

Post a Comment

0 Comments