TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

De Gea na iya koma wa Man United, City za ta ɗauki Musiala

 


.

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,

Davis de Gea

Manchester United na shirin yin mi’ara koma baya, ta hanyar neman David de Gea ya koma kulob ɗin a kan gajeren kwanturagi - wata huɗu bayan ta bari tsohon golan na ƙasar Sifaniya mai shekara 32 ya tafi a ƙarshen yarjejeniyarsa a Old Trafford. (Sun)

Manchester City na duba yiwuwar ko za ta ɗauko ɗan ƙwallon gefe na kulob ɗin Bayern Munich, Jamal Musiala, mai shekara 20. (Sport - in Spanish)

Ƙungiyar wadda ta lashe kofi uku a bara za ta fuskanci ƙalubale daga Liverpool da ita ma ke ƙoƙarin sayo ɗan ƙwallon na ƙasar Jamus. (Bild)

Bayern Munich na wasu-wasi a kan ko za ta iya ci gaba da yunƙurin ɗauko ɗan wasan FulhamJoao Palhinha a watan Janairu, bayan ta kusa kammala sayen ɗan ƙwallon tsakiyar mai shekara 28 da bazara. (Bild)

Manchester United da kuma Liverpool na bibiyar ɗan bayan ƙasar Sifaniya Robin le Normand, mai shekara 26, kuma suna iya yin yunƙurin ɗauko shi daga Real Sociedad a shekara mai zuwa. (Teamtalk)

Aston Villa ta kasance a kan gaba wajen neman ɗauko ɗan ƙwallon baya gefen dama na Atletico Madrid, Nahuel Molina, mai shekara 25, wanda ya taimaka wa Argentina ta lashe Gasar Kofin Duniya bara a ƙasar Qatar. (Fichajes)

Ana sa ran koci Jose Mourinho ɗan ƙasar Portugal zai bar Roma a ƙarshen kakar nan, kuma ɗan wasan Ingila, Tammy Abraham, mai shekara 26, zai iya bin sa, su tafi wata ƙungiya a gasar Premier  League

West Ham na iya kammala sayen Sebastian Caceres, ɗan wasan baya na tsakiya daga Club America na ƙasar Uruguay, mai shekara 24 a watan Janairua kan kuɗin da bai fi fam miliyan shida ba kacal. (Football Insider)

Manchester United da Arsenal da kuma Manchester City, na ci gaba da sa ido a kan Michael Kayode duk da yake ɗan wasan bayan tsakiya na ƙasar Italiya mai shekara 19, ya sa hannu kan sabon kwanturagi a Fiorentina. (90min)

Ian Maatsen na shirin barin Chelsea a watan Janairu, bayan ya kasa raba kansa da ɗumama benci, amma ɗan wasan na ƙasar Holland mai shekara 21 wanda ke buga gefen hagu a baya ko kuma a tsakiyar fili, ba shi da niyyar koma wa Burnley, inda ya yi zaman aro a bara. (Teamtalk)

West Ham na shirin fara neman wanda zai iya maye gurbin koci, David Moyes. (Football Insider)

Tsohon ɗan wasan bayan Girka, Sokratis Papastathopoulos, mai shekara 35, na shirin sake haɗuwa da tsohon abokin taka ledarsa na Arsenal, a kulob ɗin Real Betis, inda yake cin gashin kansa, bayan ƙarewar kwanturaginsa a Olympiakos. (Fabrizio Romano)

Tsohon ɗan wasan Barcelona kuma ɗan bayan ƙasar Mexico, Rafael Marquez ya shirya karɓar ragamar horar da ƙungiyar Barca, bayan taka rawar gani a ƙaramar ƙungiyar, a cewar tsohon abokin taka ledarsa Gerard Pique. (ESPN)

Ɗan wasan Al-Nassr kuma ɗan ƙwallon gaban Senegal, Sadio Mane, mai shekara 31, na shirin sayen ƙungiyar ƙwallon ƙafa a Faransa mai buga gasar ƙasar mai daraja ta huɗu Bourges Foot 18. (ESPN)

Post a Comment

0 Comments