TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Kai Tsaye: Kotun Koli Ta Fara Sauraron Daukaka Karar Atiku, Obi Kan Nasarar Tinubu.

A yau Litinin 23 ga watan Oktoba ne kotun ƙoli za ta saurari ƙararraki uku da ke ƙalubalantar hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa, wacce ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu. 


Masu shigar da ƙara su uku, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar LP, da kuma Allied Peoples Movement (APM), suna son kotun koli ta soke hukuncin kotun zaben shugaban ƙasa da ta tabbatar da nasarar Tinubu a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Post a Comment

0 Comments